Wani kwamandan mayakan rundunar “RSF” ta Sudan mai suna Musa Ali Ahmad ya zama mutum na karshe wanda a balle tare da mayaka 315 a tare da shi da kuma motocin yaki 50.
Musa ya bayyana cewa, ya yanke hukuncin ballewa ne bayan da ya fahimci cewa rundunar ta “RSF” tana kokarin kafa wata sabuwar gwamanti ne a Sudan.
A baya kadan wani kwamandan mai suna “Al-Nur Alhmad Adam, wanda aka fi sani da “Nur=alqubbah” ya balle a cikin watan Aprilu sai kuma wani kwamadan mai suna “Ali Rizqullah a cikin watan Mayu.
Haka nan kuma ana samun wasu fararen hula da suke tare da rundunar ta “RSF” suna ballewa, na bayan nan shi ne Faris al-Nur wanda ya kasance mai bayar da shawara ga kwamandan rundunar ta “RSF”.
A wata shaida da ya bayar ta kafafen watsa labaru Rizqullah ya bayyana yadda ake azabtar da duk wanda ya yi suka akan yadda shugabannin rundunar suke tafiyar da ita, haka nan kuma kashe wasu daga cikinsu.
Shi kuwa Adam ya bayar da labarin yadda ake daukar mayakan rundunar a cikin jiragen sama da suke ratsawa ta kasashen Chadi da kuma Ethiopia sannan su shiga cikin Sudan.
Dama dai a bayan mahukuntan kasar Sudan sun zargi wadannan kasahsen biyu masu makwabtaka da ita da cewa, suna taimakawa rudnunar ta “RSF” wacce take yaki yaki da ita.
Haka nan kuma gwmanatin ta sudan tana zargin wasu kasashen waje da su ka hada da UAE da taimakawa RSF da makamai da kuma kudade.