Search
Close this search box.

Yan Ta’addan Boko Haram Sun Sace Matafiya Tara A Iyakar Najeriya Da Nijar

Wasu rahotanni sun bayyana cewar mayakan Boko Haram sun sace wasu matafiya a yankin Kumadouku da ke kan iyakar Najeriya da Nijar. Masanin kan harkar

Wasu rahotanni sun bayyana cewar mayakan Boko Haram sun sace wasu matafiya a yankin Kumadouku da ke kan iyakar Najeriya da Nijar.

Masanin kan harkar tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagàzola Makama ne, ya bayyana hakan inda ya ce lamarin ya faru a ranar 22 ga watan Agusta, 2024.

Ta ce ’yan ta’addan su shida ɗauke da makamai, sun farmaki wasu motocin Najeriya da ke tsakanin kauyen Muria da Walada, a kusa kogin Kumadouku da ke kan iyakar Nijar, tare da yin awon gaba da fasinjoji tara.

A cewarsa, sun kai harin nd a kan dawakai, inda suka sace maza bakwai da mata biyu.

Wasu Daga cikin waɗanda aka sace sun haɗa da Kuriya Mallam Kura, daga Damasak Central, Yusufu Yau Ustass, daga Hausari Ward, Damasak, Ya’gana Malam Hassan, wata  mata, daga Damasak.

Daya daga cikin ’yan uwan waɗanda aka sace, Yusufu Ya’u Ustaz, ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen suna neman a biya su kuɗin fansa Naira miliyan biyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments