Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran (IRGC) sun bada bayanin cewa sun kakkabo jirgin yakin Amurka samfurin US MQ-1 a jiya Laraba, a lokacinda yake shawagi kan tsibirin Qeshm na tekun farisa. Wannan kuma ya kawo adadin irin wadannan jirage 15 da suka kakkabo a yankin tun bayan yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar a farkon wannan shekarar. Labarin ya kara da cewa, wannan ya nuna cewa har yanzun gwamnatin kasar Amurka bata daddara ba, kan cimma mummunan manufofinta a JMI, musamman na bude mashigar ruwa ta Hurmuz wacce take a bude kafin ta dorawa kasar Yaki.
A wani bangare kuma dakarun na IRGC sun bayyana cewa sabon tsarin garkuwan sararin samaniya na JMI yana aiki da kyau, saboda da waya wani jirgin yakin Amurka wanda ake sarrafa shi daga nesa ya tsira daga sabbin tsarin garkuwan sararin samaniyar kasar.
Daga karshe labarin ya kara da cewa Jiragen MQ-1 Predator dai dai kirar kamfanin General Atomics na ma’aikatar yakin Amurka ne. Kuma sun yi amfani da shi a kasar Afganistan a lokacinda suka mamayeta na shekaru 20, don tsananin barnansa da kisan mutane a lokacin ana kiransa mahaushin Kandahar.