Faransa: An Shiga Yajin Aikin Gama Gari Bayan Jerin Zanga-zanga

Kamar ko wane lokaci tun soma boren Gwamnati ta sanar da zuba jami'an tsaro a fadin kasar.

Kungiyoyin kwadago da dama sun kira yajin aikin gama gari da zanga-zanga a wannan Alhamis, bayan shafe makonnin uku a jere na zanga zanga a ko wacce ranar Asabar.  

Kamar ko wane lokaci tun soma boren Gwamnati ta sanar da zuba jami’an tsaro a fadin kasar.

Ma’aikatan layin dogo, dalibai, malamai, ma’aikatan gwamnati, da masu ritaya na kira da su shiga gangami a wannan Alhamis, 5 ga Nuwamba, kan matsalar tsadar rayuwa da hauhawan farashin makamashi bayan fishin da daliban makarantar sakandare suka faro yau kusan wata guda saboda matsalolin da suka dabaibaiye sha’anin daukar karatu.

Kungiyoyin kwadago suna kira ga ma’aikatan gwamnati da na masu zaman kansu, matasa, da masu ritaya da su yi gangami don neman albashi, ayyuka, ayyukan gwamnati, da masana’antu, a daidai lokacin da ake fuskantar hauhawar farashin tsadar rayuwa, rashin tsaro da kuma karuwar korar ma’aikata.

Ministan Harkokin Cikin Gida na faransa Laurent Nuñez ya sanar da cewa matakan tsaro za su kasance “daidai da na ranar 31 ga Oktoba.

A waccen lokacin an jibge jami’an tsaro 70,000 a duk fadin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted