Ministan Harkokin Wajen Jamus Ya Goyi Bayan Yaki Kan Iran

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya zargi ministan harkokin wajen Jamus da goyon bayan yake yaken da Amurka da HKI suka kaiwa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya zargi ministan harkokin wajen Jamus da goyon bayan yake yaken da Amurka da HKI suka kaiwa kasar Iran, ba tare da lura da matsalolin tattalin arziki da kuma na rayukan mutanen da aka sauya a yake yaken.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakal Baghaei yana fadarhaka a shafinsa na X, yana kuma fadar cewa, ministan ya goyi bayan Amurka da HKI kan yake yaken da suka dorawa JMI ba tare da ya yi tunanin abinda zai faru da Iraniyawan da za’a kashe da kuma asarorin rayuwa da dukiyoyin da ke cikinsu ba.

Baghaei ya ce, akwai wani lokacinda chancellor Friedrich Merz yake fada dangane da yakin da Amurka da HKI suka dorawa Iran kan cewa suna yin mummunan aiki a madadimmu.Amma bayan yan watanni da yakin Merz yaa ce kasashen Turai sun yi asarar euro billion 100 saboda yakin. Amma a halin yanzun kuma ministan harkokin wajensa yana cewa yaki kan Iran dai dai ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted