Rundunar Sojojin Sama ta Iran ta kaddamar da wani harin makamai masu linzami da na jiragen sama marasa matuki a kan sansanonin sojojin Amurka na Al-Riffa da Awali da ke Bahrain.
A cewar wata sanarwa da IRGC ta fitar, ta ce an kai harin ne a matsayin martani kai tsaye ga ci gaba da keta sararin samaniyar Iran da jiragen saman Amurka marasa matuki suka yi da kuma wasu ayyukan Amurka na kiyayya kan Iran.
Sanarwar ta ce an kai hari kan na’urorin rada- rada guda biyu mallakar tsarin tsaron sararin samaniyar Patriot na sojojin Amurka, wadanda aka tura a sansanonin Al-Riffa da Awali da ke Bahrain, a matsayin martanin.
IRGC ta ce wannan ya zo ne bayan da jiragen leken asiri na MQ-1 da MQ-9 guda biyu da jiragen sama marasa matuki suka keta sararin samaniyar Iran, wanda hakan ya sa Rundunar Sojojin Sama ta IRGC ta kai hari kan sansanonin sojojin Amurka a sansanonin biyu.
Sanarwar ta yi gargadin cewa sararin samaniyar Iran jan-layi ne ga Sojojin kasar kuma hakan fuskanci martani mai karfi.
Wannan sabon hari shi ne martani na uku da Iran ta mayar a cikin ‘yan kwanakin nan kan muradun Amurka da ke Bahrain, wanda ke dauke da daya daga cikin manyan rundunonin sojojin Amurka a Tekun Fasha, ciki har da hedikwatar Rundunar Sojan Ruwa ta Biyar ta Amurka.