Araqchi: Sai An Biya Bukatun Iran Kafin Bude Mashigar Hormuz

Ministan Harkokin Wajen Iran dangane da magana game da sake bude mashigar ruwa ta Hormuz, ya jaddada cewa babu ma’ana matukar ba a biya buƙatun

Ministan Harkokin Wajen Iran dangane da magana game da sake bude mashigar ruwa ta Hormuz, ya jaddada cewa babu ma’ana matukar ba a biya buƙatun Iran ba

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Sake bude mashigar Hormuz ba zai yiwu ba, sai an biya buƙatun Iran, yana mai jaddada cewa: Iran yayin da take shirin kare kanta, har yanzu tana bude tattaunawa.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen wani taron da aka gudanar domin murnar Ranar Ƙasa ta Oman, Araghchi ya yi tsokaci kan ziyarar tawagar Qatar a Tehran, inda ya bayyana cewa ziyarar ba abin mamaki ba ce. Ya bayyana cewa masu shiga tsakani tsakanin Iran da Amurka kan yi ta zirga-zirga akai-akai tsakanin ɓangarorin biyu, suna isar da ra’ayoyi da shawarwari a lokacin tarurrukan da suke yi.

Ya kara da cewa, “Matsayin Iran a bayyane yake: sai dai idan an biya buƙatunta, batun mashigar Hormuz da sake bude ta ba za a tattauna ba.” Ya sake nanata cewa: Iran ta sha bayyana shirinta na kare kanta da kuma shirinta na shiga tattaunawa.

Dangane da dangantaka tsakanin Tehran da Muscat, Ministan Harkokin Wajen Iran ya lura da kusancin da ke tsakanin kasashen biyu, wanda koyaushe ya dogara ne akan girmama juna. Ya yaba da manufofin harkokin wajen Oman a matsayin masu tasiri da kuma ci gaba da kokarin rage tashin hankali, kuma ya tabbatar da hadin kai tsakanin bangarorin biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted