Qalibaf: Manufar Amurka Ita Ce Wawure Albarkatun Yankin

Shugaban Majalisar Dokokin Iran ya bayyana cewa: Manufar Amurka ita ce ta wawure albarkatun ƙasashen yankin Tekun Farisa Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran (wato

Shugaban Majalisar Dokokin Iran ya bayyana cewa: Manufar Amurka ita ce ta wawure albarkatun ƙasashen yankin Tekun Farisa

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran (wato Majalisar Dokokin Kasar) Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Amurka na ci gaba da kulla dangantaka da kasashen yankin kogin Farisa da kuma yankin Gabas ta Tsakiya da nufin wawure albarkatunsu.

A ranar Laraba da rana, ranar farko ta ziyararsa a Iraki, Muhammad Baqir Qalibaf tare da rakiyar tawagar ‘yan majalisar dokokin Iran, ya gana da shugaban kasar Iraki Nizar Amidi don tattaunawa kan batutuwa asu yawa.

A farkon taron, Qalibaf ya ce, “A madadin shugaban Iran da al’ummar kasar, musamman Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, yana ganin ya zama wajibi ya bayyana godiya da jinjinarsu ga kasancewar jami’an Iraki a Iran don halartar jana’izar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci. Ya kuma mika godiya ga miliyoyin mutane, wadanda suka kai miliyan goma, wadanda suka halarci jana’izar Jagoran Juyin Juya Halin na Musulunci a Iraki.”

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya kara da cewa: Kasashen biyu sun tsaya tare a cikin mawuyacin hali, yana mai tunawa da cewa wani mutum kamar Saddam Hussein, ta hanyar makirci da cin amana na Amurka, ya aikata laifuka a kasashen biyu. Duk da haka, al’ummomin ƙasashen Iran da Iraki suka tsaya tare da juna a lokacin da ya biyo bayan Saddam, da kuma a cikin mawuyacin lokaci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted