A daidai lokacin da yakin Gaza yake cika kwanaki 170 da barkewa, ‘yan gwgawarmaya sun harba makamai linzami zuwa matsugunan da suke kusa da Gaza.
Dakarun “Sarayal-Quds’ dake karkashin kungiyar Jiahdul-Islami ta sanar da harba makamai masu linzamin zuwa kan matsuganan ‘yan share wuri zauna.
A gfe daya kuma ana cigaba da fafatawa a tsakanin ‘yan gwgawarmaya da sojojin mamaya a kusa da asibitocin “Khan-Yunus”, “Amal’ da Nasir.
Kwakanin kadan da su ka gabata ne dai sojojin HKI su ka yi kutse a cikin asibitin al-sahfa tare da tashin gobara a cikin dakunan da ake yin tiyata. Bugu sun yi harbe-harbe da su ka yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa da dama.