Yamen : Ansarullah Ta Gargadi Kasashen Musulmi Kan Makircin Da Amurka Da Isra’ila Ke Kullawa

Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya gargadi kasashen musulmi kan makircin da Amurka da Isra’ila suke kullawa na sake fasalin yammacin Asiya, yana mai

Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya gargadi kasashen musulmi kan makircin da Amurka da Isra’ila suke kullawa na sake fasalin yammacin Asiya, yana mai bayyana su a matsayin makiyan al’ummar musulmi gaba daya.

Adbul-Malik al-Houthi ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi ta gidan talbijin a yammacin ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa, “Maganar Washington da gwamnatin Tel Aviv na samar da sabuwar Asiya ta yamma ta shaida makircinsu da nufin kai wa al’ummomin yankin da kasashen yankin hari.”

Ya bayyana cewa, yahudawan sahyoniya na zaman wata barazana ta hakika ga daukacin al’ummar musulmin duniya, wadda ta ketare dukkanin mazhabobi, akidu, da kuma alakarsu.

“Makircin Amurka da Isra’ila na da nufin hana al’ummar musulmi samun duk wani nau’i na kariya da kare kansu.

Har ila yau Houthi yana mai jaddada cewa wajibi ne musulmi su dauki matakin dakatar da laifukan da Isra’ila ke yi a yankunan Falasdinawa da ta mamaye da kuma wadata Falasdinawa da kayayyakin masarufi da kayan agaji.

Da ya koma kan abubuwan da ke faruwa a Siriya, shugaban kungiyar Ansarullah ya ce sojojin Isra’ila sun fito fili sun yi watsi da dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya a lokacin da suke kai hare-hare a wasu muhimman wurare a fadin kasar ta Siriya.

“Ayyukan wuce gona da iri na Isra’ila kan Siriya, wadanda aka yi ba tare da wani hukunci ba, tare da goyon bayan Amurka, wani bangare ne na yunkurin gwamnatin kasar na kuntatawa al’ummar musulmin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments