Mai shari’a Janet Vargas a wata kotu dake unguwar Manhattan ta yanke hukuncin cewa matakin da gwamnatin Donald Trump ta dauka na dakatar da bayar da izinin shiga cikin Amurka ga ‘yan kasashe 75 da cewa ba ya bisa doka,kuma daukar mataki irin wannan ya fi karfin ikon ministan harkokin waje Marco Rubio.
Mai shari’ar da ta yanke hukunci a jiya juma’a ta kuma ce; Siyasar da ma’aikatar harkokin waje ta sanar a watan Janairu,” Ta sabawa doka a fili” kuma “Tana cin karo da dokar yin hijira ta gwamnatin tarayya wacce ta raba minista da hakkin daukar mataki irin wannan akan visa ta shiga cikin kasar.
Gwamnatin ta Donald Trump dai ta dauki matakan hana ‘yan wasu kasashe 75 hakkin shiga cikin kasar Amurka da su ka fito daga nahiyar Afrka, yankin Caraebia, gabas ta tsakiya da Kudancin Asiya. Haka nan kuma hanin shiga cikin Amurkan ya shafi kasashen Balkan da Latin na Amurka.
Amurka ta fake da cewa mai mafi yawancin mutanen da suke fitowa daga cikin wadannan kasashen, suna zamarwa Amurka wani nauyi ne da yake mayar da su zama masu sarrafa muggan kwayoyi.
Kotun ta Manhattan ta yanke hukunci akan rashin dacewar matakin na gwamnatin Trump da doka, bayan da wasu kungiyoyi biyu na bakar fata da kuma masu kare hakkokin ‘yan hijira Mabiya Roman katolika su ka shigar da kara. A cikin watan Janairun a wannan shekarar ma’aikatar harkokin wajen Amurkan ta sanar da yin watsi da bukatar shiga cikin Amurka ta mutane 100,000 wanda ba a taba yin kwatankwacinsa ba.