Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar hizbullaha ta kasar Labanon ta bayyana kasar Amurka a matsayin shugabar yan ta’adda ta duniya, bayan da Amurka ta kakakabawa kungiyar sabon takunkumi inda ta zargeta da ce dakarun kare juyin musulunci na iran ne ke juya alamuranta.
A cikin wani jawabi da kungiyar ta fitar a jiya jumaa hizbullah ta yi watsi da ikirarin na trump kuma ta bayyana mataki a matsayin wani yunkuri ne na matsin lamba kan kungiyar da nufin kare HKI yadda za ta ci gaba da mamaye kudancin labanon da kuma share mata hanya yadda za ta ci gaba da cimma manufofinta a yankin.
Haka zalika hizbullah ta kare alakarta da Tehran inda ta ce Muna girmama dangatarka ta kud da kud dake tsakaninmu da Iran kuma muna alfahari da ita.
A cikin bayanin tace iran ta tsayawa kasar Labanon ta nuna mata goyon baya kuma ta taimaketa wajen yanto kasarta da kuma dawo da yancinta da hakkokinta , kuma ta ci gaba da kasancewa tare da ita a dukkan matakai da rikice-rikice ciki har da bayar da gudunmawa na sake gina kasar bayan yakin isra’ila na shekara ta 2006