Ministan Harkokin Wajen Iran ya mayar da martani ga ikirarin Amurka game da kakaba takunkumin tattalin arziki mafi muni a tarihi kan Iran
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi, wanda ke mayar da martani ga ikirarin Amurka na yakin kakaba takunkumi mafi barna a tarihi, ya yi ikirarin cewa wannan yanayi mai maimaitawa zai gaza.
Araqchi ya rubuta a cikin wani rubutu a dandalin “X” cewa:
Shekaru 14 da suka gabata: Takunkumin da Amurka ta ce shi ne ya fi tsauri a tarihi ya gaza cimma burinsa kan Iran.
Shekaru 8 da suka gabata: Matsin lamba mafi girma da ta dauka kan Iran ya gaza cimma manufofinsa.
Watanni 5 da suka gabata: Yakin wuce gona da iri da Amurka ta kakaba wa Iran, bai Sanya Iran ta kai ga mika wuya ba tare da gindaya sharaɗi ba ya gaza, don haka makirce-makircen Amurka ba zasu taba mafita gare ta ba.