Rahotanni na cewa Hukumar Kula da Harkokin Wasanni ta Najeriya ta bai wa dukkan mambobin Kwamitin koli da ke jagorancin hukumar kwallon kafa ta kasar wa’adin sa’o’i 24 da su ajiye aikinsu.
Manyan jami’an hukumar kwallon ƙafar Najeriyar da ke karkashin jagorancin Ibrahim Gusau, na fuskantar wannan matsain lambar ce biyo bayan tuhume-tuhumen da ake musu na kasa sauke nauyin da aka dora musu, ciki har da almundahana, lamarin da janyo tabarbarewar sha’anin kwallon kafa a Najeriya.
Idan za a iya tunawa a ranar 16 ga watan Nuwamban shekarar bara ta 2025 tawagar kwallon kafar Najeriya Super Eagles ta kasa samun tikitin buga gasar cin kofin Duniyar da ta gudana a Amurka da Canada da Mexico, bayan rashin nasara a hannun Jamhuriyar Congo.
A cikin wannan wata na Agusta kuma tawagar kwalllon Najeriyar ta mata Super Falcons, itama ta gaza samun tikitin halartar gasar cin kofin Duniya ta matan da za a yi a Brazil, karo na farko tun bayan fara gasar a shekarar 1991.
Wasu bayanai dai sun ce umarnin ajiye aiki da aka bai wa shugaban NFF Ibrahim Gusau da tawagarsa ya biyo bayan ganawar da aka yi tsakanin jagorancin hukumar kula da wasanni ta Najeriya NSC da kuma fadar shugaban ƙasa.