A nan Iran an gudanar da taron ranar duniya ta tunawa da mutanen da ayyukan ta’addanci su ka cutar da su wanda ya sami halartar shugaban cibiyar Nazari da bincike na siyasar kasa da kasa, da shugaban bangaren kasa da kasa na ma’aikatar shari’a da kuma babban sakataren cibiyar kare hakkin bil’adama da kungiyar iyalan shahidai da wadanda su ka kwanta dama da cutuwa saboda ayyukan ta’addanci.
Daga cikin mahalarta taron da akwai iyalan daliban makarantar “Minab” da su ka yi shahada sanadiyyar ta’addancin Amurka.
Daga cikin jawaban da aka gabatar an yi kira da a mayar da hankali wajen bayani akan fuskokin ‘yan adamtaka da hakkin dan’ada da sakon da hakan yake tattare da hakan ga al’ummu mabanbanta.
Bugu da kari, an kaddamar da wani littafi mai taken: “Rahotanni Akan Shekarar Ta’addanci 2025.”
Majalisar Dinkin Duniya ce ta ayyana ranar 21 ga watan Ogusta a matsayin ranar wayar da kai akan ayyukan ta’addanci ta duniya.” A kowace shekara ana yin taruka domin girmama wadanda ‘yan ta’adda su ka kashe, ko su ka cutar da su.
An fara raya wannan ranar ne a 21 ga watan Ogusta na 2018.
Majalisar Dinkin Duniyar tana yin rika da rika mayar da hankali wajen biyan bukatun iyalan wadanda aka cutar da su ta hanyar ayyukan ta’addanci.