Hamas: Kisan Gilla Ba Zai Karya Zukatan Yan Gwagwarmaya Ba

kisan gilla kamu da kullewa ba zai iya raunana zukatan yan gwagwarmaya ba

kungiyar gwagwarmaya ta hamas ta yi tir da matakin da sojojin isra’ila suka dauka na harbin wani bafalasdine a garin jenin dake arewacin kogin jodan da aka mamaye, ta jaddada cewa kisa ko kamu da dauri ba zai ta ba karya zukatan yan gwagwarmayar falasindu  ba, ko kuma ya girgiza su yasa su yi rauni.

Kungiyar dake yankin gaza a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya jumaa ta yi jimamin shahadar Fathi hazem mai shekaru 58 da haihuwa wanda yayi shahada sakamakon raunuka da ya samu bayan da sojojin isra’ila suka harbe shi da safiyar juma’a, ta ce zabin falasdinawa na kin amincewa da mamayar isra’ila zai ci gaba da tsananta kuma ba za su canza ba

Haka zalika kungiyar hamas ta yi kira ga matasa falasdinawa masu ta sowa a yankin gabar yammacin kogin Jodan da su ci gaba da dagewa kan nuna kiyayya da mamayar Isra’ila , kuma su tunkari sojojin isra’ila kan mamayar yankunansu da suke yi domin wannan shi ne kare kasar falasdinu da kuma yancinsu

Ana ta bangaren itama kungiyar gwagwarmaya ta jihadil islami tayi tir da matakin da sojojin isra’ila suka dauka a jenin na kashe Hazem a gaban iyalansa kuma sun bayyanashi a matsayin kisan kai na daukar fansa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted