Jami’an ‘Yan Sandan Afirka Ta Kudu  sun Kama Manyan Dillalan Muggan  Kwayoyi Biyar

Jami'an 'yan sanda kasar Afirka ta kudu kama wasu mutane 5 wadanda ake zargin da cewa suna tafiyar da kasuwancin muggan kwayoyin da kudinsu sun
Hoton 'yan sanda da masu laifi

Jami’an ‘yan sanda kasar Afirka ta kudu kama wasu mutane 5 wadanda ake zargin da cewa suna tafiyar da kasuwancin muggan kwayoyin da kudinsu sun kai Dala miliyan 37.

Mutanen da aka kama suna tafiyar da wata boyayyar masana’anta ta mugaggan kwayoyi a yankin Limpopo a yayin wani samame da su ka kai a yankin.

‘Yan sandan kasar ta Afirka ta kudu sun kuma bayyana cewa; A yayin da su ka kai harin sun gano tsararren kamfani da aka kafa domin samar da muggan kwayoyi masu hatsari.”

Majiyar ‘yan sandan ta kuma kara da cewa; mutanen da aka kama shekarunsu suna a tsakanin 20 ne zuwa 47,sun kuma hadi ‘yan kasashen Maxico biyu, ‘yan kasar Zambawe biyu da kuma dan kasar Malawi.

Rahoton cibiyar da take fada da tsararrun laifuka a duniya, ya ce: “Kasar Afirka Ta Kudu tana cikin inda aka fi sarrafa kwayar “Meth” kuma kasuwarta tana kara bunkas zuwa kasashen da suke makwabtaka da ita.”

A shekarar 2025 rahoton cibiyar ta bayyana cewa; yadda ake samun karuwar masana’antun muggan kwayoyi a Afirka ta Kudu  da Mozambique, yana nuni da karuwar kutsen da masu sana’ar wadannan muggan kwayoyin  daga yankin Latin na Amurka suke kara kutse cikin nahiyar Afirka

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted