Jiragen Ruwa Sun Kama Da Wuta A Mashigar Ruwan Hormuz

Gobara ta tashi a kan manyan jiragen ruwa guda biyu da suka karya dokoki a gabashin mashigar ruwan Hormuz Ofishin Hulɗa da Jama’a na Rundunar

Gobara ta tashi a kan manyan jiragen ruwa guda biyu da suka karya dokoki a gabashin mashigar ruwan Hormuz

Ofishin Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojan Ruwa ta Iran ya sanar da cewa: Jiragen ruwa biyu masu ɗauke da mai sun kama da wuta bayan sun fuskanci hari kan daga wasu nakiyoyin ruwa a gabashin mashigar ruwan Hormuz.

Ofishin Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojan Ruwa ya bayyana cewa: Jiragen ruwan biyu sun shiga yankin da aka hana zirga-zirgar jiragen ruwa a gabashin mashigar ruwan Hormuz a safiyar yau, duk da gargadin da aka yi a baya. Bayan an kashe tsarin tantancewa da na jagorantar tafiyarsu, sun bi takan nakiyar ruwa lamarin da ya yi sanadin kamawarsu da wuta. Ofishin Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojan Ruwa ya jaddada cewa: Masu jiragen ruwa, masu aiki da matukan jiragen ruwa waɗanda suka yi watsi da gargaɗin kuma suka yi tafiya a wuraren da aka hana zirga-zirgar jiragen ruwa bayan sun an kashe tsarin zirga-zirgar jiragen ruwa suna da alhakin kai tsaye kan sakamakon duk abin da zai janyo lalacewar jiragen ruwansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted