Rahoton Yakin Kan Iran Ya Janyo Wa Amurka Mummunar Hasara

Rahoton yaki kan Iran yana kara janyo lalacewar al’amura ga Amurka ta fuskoki da dama Wani rahoto da Cibiyar Nazarin Dabaru ta Ostiraliya ta Lowy

Rahoton yaki kan Iran yana kara janyo lalacewar al’amura ga Amurka ta fuskoki da dama

Wani rahoto da Cibiyar Nazarin Dabaru ta Ostiraliya ta Lowy (LEI) ta fitar ya nuna cewa: Rikicin da ke faruwa tsakanin Amurka da Iran, wanda ya fara a watan Fabrairun da ya gabata, ya raunana karfin sojojin Amurka saboda raguwar tarin makamai masu linzami masu cin dogon zango.

A cewar rahoton, Amurka ta ci gaba da kasancewa a matsayi mafi girma da maki 78.9 cikin 100, yayin da China ta zo ta biyu da maki 73.6. Bambancin da ke tsakanin kasashen biyu maki 5.3 ne kawai, mafi kankanta tun lokacin da aka fara wannan nau’in binciken.

Dangane da karfin soja, Amurka ta samu maki 87.4, idan aka kwatanta da maki 72.1 ga China.

Rahoton ya nuna cewa: Rikicin da ke faruwa tsakanin Amurka da Iran, wanda ya fara a watan Fabrairun da ya gabata, ya raunana karfin sojojin Amurka saboda raguwar tarin makamai masu linzami masu cin dogon zango.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted