Mataimakin majalisar koli da malaman shia a kasar Lebanon Sheikh Ali –Al-Khadib ya bayyana cewa, turjiya da kuma nasarar da JMI ta samu kan Amurka da HKI sun taimaka wajen dawo da zaman lafiya a yankin Asia.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sheikh Ali Al-Khadib yana fadar haka a jiya Asabr, a taron manya manyan bakin JMI na Jana’izar Imam Shahid Khaminaei anan Tehran.
Sheikh Khadib ya bayyana cewa, da Allah ya kiyaye, Iran bata sami nasara a wannan yakin ba, da kuwa HKI zata ci gaba da mamayar sauran kasashen larabawa makobtanta. Dangane da kasar Lebanon kuma Sheikh Al-Khadib ya godewa JMI dangane da taimakon da take bawa kungiyar hizbulla a fafatawar da take da HKI.
A ganawarsa da Aya. Reza Ramadani sakataren kungiyar Ahlulbaiti ta duniya Khadib y ace mutanen Lebanon sun yi hakuri sun kuma sha wahala a hannun yahudawa sahyoniyya amma shigowar kasar Iran ya taimaka wajen rage yawan matsalolin da yan shia a kasar Lebanon suke fuskanta.