Miliyoyin Mutane A Birnin Tehran Sun Gudanar Da Sallar Jana’izar Gawar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci

Miliyoyin mutane a birnin Tehran sun gudanar da sallar jana’iza  ga gawar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci da ya yi shahada Miliyoyin masu alhini sun

Miliyoyin mutane a birnin Tehran sun gudanar da sallar jana’iza  ga gawar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci da ya yi shahada

Miliyoyin masu alhini sun yi sallar jana’izar gawar Imam Ayatullah Seyyed Ali Khamenei da ya yi shahada, tare da tarin tawagar iyalansa, a wani gagarumin biki da ya samu halartar manyan jami’ai, sojoji, da kuma jama’ar kasa.

Ya’yan jagoran shahidin sun halarci gudanar da jana’izar da aka gudanar a Masallacin Imam Khomeini da ke birnin Tehran, inda suka isa mintuna kafin fara juyayin.

Shugabannin sassa uku na gwamnatin Iran sun kuma halarci juyayin jana’izar a Masallacin Imam Khomeini da ke Tehran don halartar alhinin shahidan Iran.”

Ayatollah Jafar Subhani ne ya jagoranci sallar jana’izar, a cikin yanayi na bakin ciki da alhin, kuma tare da halartar jama’a da dama da suka halarci juyayin bankwana ga gawawwakin wadanda suka yi shahadan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted