Sojojin Iran Sun Bayyana Cewa; Taron Jana’izar Jagora Shahidi Ya Farkar Da Duniya Akan Fada Da Masu Girman Kai

Mai Magana da yawun sojan Iran Amir Akrami Niya ya bayyana cewa; Al’ummar Iran ta kafa tarihi saboda yadda su ka fito a cikin miliyoyi

Mai Magana da yawun sojan Iran Amir Akrami Niya ya bayyana cewa; Al’ummar Iran ta kafa tarihi saboda yadda su ka fito a cikin miliyoyi domin yin bankwana da jagoran juyi shahidi Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

Haka nan kuma ya ce abinda yake faruwa  ya sauya zuwa wani yunkuri na farkar da al’ummar duniya akan fada da zalunci da girman kai.

Kakakin sojan na Iran dai ya bayyana hakan ne a yau Litinin a wurin taron bankwada da ake yi wa gawar jagora shahidi Ayatullah Sayyi Ali Khamenei.

Haka nan kuma ya nuna fatansa na ganin al’ummun duniya musamman raunana sun yunkura domin kalubalantar azzalumai da masu girman kai na duniya, da kuma yin tafiya akan tafarkin gwagwarmaya na fuskantar masu danniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted