Gwamnatin kasar ta bada sanarwan cewa, ba zata taba yin kasa a guiwa ba, wajen neman fansar jinin Imam Shahid Aliyul Khaminaei ba. Wanda sojojin Amurka suka kashe a farkon yakin Ramadan na shekara ta 1447.
Tashar talabijan ta presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Amir Hatami babban kwamandan sojojin kasar Iran ne ya na fadar haka a yau Lahadi kuma bayyana haka ne bayan sallar jana’izar da aka yiwa imam Sayyid Aliyul Khaminaei (q) da iyalan gidansa.
Yace: wadanda suka aikata kissan Imam Shahid su san cewa, Iraniyawa da kuma mu jami’an tsaron kasar ba zamu taba manta da gibin da suka yi mana watanni 4 da suka gabata ba. Kuma zamu dauki fansar jinin Shahidammu a lokacin da ya dace.
A ranar 28 ga watan Fabarairu na shekara ta 2026 ne sojojin Amurka da HKI suka kai hare hare ta sama a kan gidan Jagoran a nan birnin Tehran, inda suka kashe shi da kuma wasu daga cikin iyalan gidansa.
Imam Aliyul Khaminaei, wanda yayi shahada yana dan shekara 86 a duniya, shi ne mutum na biyu a daraja bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran a shekara 1979. Imam Khomainei (q) ya kafa JMI shi kuma ya ginta ta.
Ya rike manya manyan mukaman gwamnati bayan nasarar juyin juya halin, daga ciki an zabe shi kan kujerar shugabancin kasar na shekaru 4, 4 har sau biyu. Sannan ya zama jagoran juyin juya halin musulunci na tsawon shekara 37.