Mahalarta makokin shahadan jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran sun yi rera taken mutuwa ga Amurka da Isra’ila!
Mahalarta makoki a jana’izar Ayatollah Ali Khamenei sun yi rera taken adawa da kiyayyarsu ga Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta Yahudawan Sahayoniyya .
Zainab Abdul-Jabbar, wakiliyar Gidan Talabijin na Al-Alam a Masallacin Imam Khomeini, ta ruwaito cewa: An yi jana’izar Ayatullahi Sayyid Ali Khamenei da ya kunshi dimbin jama’a daga ko’ina cikin kasar.
Wakiliyar ta tabbatar da cewa: Masu makokin sun yi ta rera taken “Mutuwa ga Amurka” da “Mutuwa ga Isra’ila” kuma sun sake sabunta alkawarinsu na mubaya’a ga sabon Jagoran Addini Ayatullah Mojtaba Khamenei.