Miliyoyin mutanen kasar Iran daga ciki da kuma wajen kasar ne suka halarci sallar Jana’izar Imam Sayyid Aliyul Khaminaei shahici a yau Lahadi a musallah ta Imam Khomainei (q) dake nan Tehran.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, Aya. Jaafar Subhani daga daga cikin manya manyan malaman addinin a kasar ne ya jagoranci sallar Jana’izar.
Labarin ya kara da cewa a dai dai lokacinda cikin musallar ta cika jami’an tsaro sun rufe kofofin shiga wurin har zuwa bayan sallah. Amma hatta hanyoyi da suke hade da masallacin ko ta ina sun ciki da mutane, wasu da dama basu sami sallar ba saboda cinkoson mutane da kuma hana ababen hawa na jama’a isa kusa da masallacin saboda tsaro.
Labarin ya kara da cewa an yi sallar har kasha Uku, daya ta Jagora shahidi, daya kuma ta sayyida Bushra Hussaini Khaminaei, sai kuma na Shahidi Mesbahul Huda Baqiri kani, da Zahra Haddad Adal, Matar sabon jagora Ayatullahi sai kuma na ukku ta Zahra Mohammadi Golpayegani jikan Jagoran.
A ranar Talata za’a kai gawawwakin birnin Qom sannan sannan ranar Alhamis kuma Mashahd inda za’a yi masu makwanci na karshe a gefen hubbaren Imam Arrida (a).