A wani sabon harin da ‘yan sahayoniya su ka kai a cikin birnin Gaza, mutane 2 sun yi shahada, yayin da wani mutum daya ya yi shahada a Khan-Yunus.
Bugu da kari harin na ‘yan sahayoniya ya yi sanadiyyar jikkatar wasu mutane 20 a birnin na Gaza da kuma Yanin Muwasi dake Khan-Yunus.
Majiyar Asibiti ” Ash-shifa” ce ta sanar da adadin shahidan a cikin birnin Gaza bayan harin da sojojin sahayoniya su ka kai a kan titin Umar Mukhtar.
Haka nan kuma wani jirgin sama maras matuki samfurin ” Quad-copter” ya jefa bama-bamai a yankin Arewacin Gaza a sansanin ‘yanhijira na “Shati” da ya yi sanadiyyar jikkata masunta uku, kuma tuni an dauke su zuwa asibiri.
Wadannan hare-haren dai suna zuwa ne duk da cewa an tsagaita wutar yaki alhali an fara aiki da shi ne tun a ranar 11 Oktoba na shekarar da ta gabata.
Ma’ikatar kiwon lafiya ta sanar da cewa;Irin wadannan hare-haren da HKI bayan tsagaita wutar yaki, sun yi sanadiyyar shahadar mutane 1066, da kuma jikkata wasu 3445.