Miliyoyin mutanen Iran sun cika titunan birnin Tehran domin isa dandalin ” ‘Yanci” domin sake jaddada bankwana da jagora shahidi da kuma uku daga cikin iyalansa.
Tun da jijjfin safiyar yau ne dai mutanen Tehran da kuma na wasu garuruwa da suke kusa su ka rika kwarara a cikin mayan tituna saboda isa birnin na “‘yanci”, yayinda wasu su ka yi wa gawar shahidin rakiya daga babban masallacin “Imam Khumaini”.
Tashar talabijin din ‘almayadin” ta bayyana cewa; yadda aka cika kwanaki 4 a jere mutane suna fitowa domin yin bankwana da shahidin yana kara tabbatar da cewa, ba za yi bar jinanen shahidan su tafi haka siddan ba.
Tun a ranar Juma’a ne dai aka fara zaman bankwana da jagora shahidi a masallacin Imam Khumaini da tawaga ta kasashen waje su ka fara halarta. Daga ranar Asabar kuwa zuwa yau mutanen gari ne suke yin bankwana da shi.
Ana sa ran cewa a gobe Talata za a tafi da gawar jagora shahidi zuwa birnin Qum, daga can kuma za a wuce da shi zuwa birane Najaf da Karbala. A ranar Alhamis ne dai za a binne gawar shahidin a hubbaren Imam Ridha ( a s.) da shi ne Imami na 8 a jerin imamai 12 na iuyalan gidan Manzon Allah ( s.a).