Senegal ta aike da wakilinta na musamman a jamhuriyar Nijar don isar da sakon shugaba Bassirou Diomafaye ga Firaminisata Ali Lamine Zeine da kuma shugaban mulkin sojin kasar Janar Abdurahmane Tiani.
Da ya ke ganawa da manema labarai, Chiekh Niang, ya ce ya kawo ziyarar don bibiyar kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasarsa da Jamhuriya Nijar tun bayan da suka samu ƴancin kai daga turawan mulki mallaka.
Haka, jami’in ya tunatar kan mawuyacin hali da alakar kasashen yammacin Afirka ke ciki tun bayan da kawancen AES ya fice daga kungiyar raya tattalin arzikin yankin ECOWAS a shekara 2024.
Cheikh Niang, wanda kasarsa ke rike da shugabancin karba karba na kungiyar ya ce suna mutunta zabin kasashen sannan a shirye su ke a yi aiki tare cikin mutunci da mutuntawa.