Mai ba da Shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Nasarar ‘yan Democrat ko kuma ta ‘yan Republican da suka rage a kan mulki ba za su canza lissafin kasar Iran ba
Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Muhammad Mukhbir ya jaddada cewa: Nasarar ‘yan Democrat ko kuma ikon ‘yan Republican a Amurka ba zai canza lissafin Iran ba, kuma yana nuna rashin wayo a ce Iran zata danganta makomarta da Amurka.
A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, Mukhbir ya rubuta a Shafin dandalinsa na X cewa: “Nasarar jam’iyyar Democrat ko ikon Republican ba zai canza lissafin Iran ba, kuma ba zai yiwu Iran ta danganta makomarta da Amurka ba.”
Mukhbir ya kara da cewa: “Yakin rage karfin yana nufin kara karfin yakin ne, kuma bai kamata Iran ta zuba ido ta zama ‘yar kallo ba kawai, a’a, zata ba za karfinta na samar da kayayyaki da karfafa harkar tattalin arziki.”