Sojojin Iran sun sanar da tarwatsa wani jirgin ruwan dakon mai da ya karya dokoki a gabashin mashigar ruwan Hormuz
Rundunar sojin Iran ta sanar da cewa: Sojojinta sun tarwatsa wani jirgin dakon mai da sakamkon haka ya kama da wuta a gabashin mashigar ruwan Hormuz saboda rashin mutunta doka.
Kamfanin dillancin labaran Mehr ya ruwaito cewa: Ofishin hulda da jama’a na rundunar sojin ruwan Iran ya sanar da cewa: “A safiyar yau, wani jirgin dakon mai da ya yi kokarin keta doka da gujewa masu tsaron ruwa ta hanyar bin wata kafa da aka hana binta ya fuskanci mayar da martanin sojojin Iran da ya kai ga kamawa da wuta gami da taka wata nakiya a gabashin mashigar ruwan Hormuz.”
Sanarwar ta kara da cewa: “Mashigar ruwan Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a rufe tare da tsaurara matakan hana keta dokar daga jiragen ruwa har sai an kawar da dukkan barazana.”