Venezuela: An ayyana zaman makoki na kwanaki bakwai bayan girgizar kasa

Shugabar riko a Venezuela Delcy Rodriguez ta ayyana zaman makoki na kwanaki bakwai na kasa daga ranar Laraba, don girmama wadanda suka ras arayukansu a

Shugabar riko a Venezuela Delcy Rodriguez ta ayyana zaman makoki na kwanaki bakwai na kasa daga ranar Laraba, don girmama wadanda suka ras arayukansu a girgizar kasa da ta abkawa kasar.

 Alkalumman da aka fitar a kwanan nan, sun ce kusan mutane 2,300 ne suka rasa rayukansu sanadin girgizar kasar.

Mutane sama da 50,000 ne suka bata ko kuma ba a san inda suke ba yayin da kungiyoyin ceto ke ci gaba da bincike a cikin tarkacen dubban gine-gine da suka ruguje da kuma wadanda suka lalace, tare da fatan samun karin wadanda suka tsira da rayukansu.

Hukumar NASA ta ba da rahoton cewa gine-gine 58,870 sun ruguje ko sun lalace.

Hukumar Lafiya ta Duniya na fargabar barkewar cututtuka da rushewar ayyukan kiwon lafiya.

Girgizar kasar mai girman 7.5 ta yi mummunar barna a Caracas da wasu jihohin bakin teku, ciki har da La Guaira, Carabobo, Miranda, Aragua da Falcon.

Dubban mutane sun rasa matsugunansu, wanda hakan ya kara sanya matsin lamba ga ayyukan gaggawa da ayyukan agaji.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted