‘Yan Jarida 600 daga ketare zasu halarci tarurukan jana’izar Shahid Khamenei

Hukumomi a Iran sun ce ‘yan jarida daga kafafen yada labarai 600 ake sa ran zasu halarci tarurukan jana’izar jagoran Juyin Juya halin Musulinci na

Hukumomi a Iran sun ce ‘yan jarida daga kafafen yada labarai 600 ake sa ran zasu halarci tarurukan jana’izar jagoran Juyin Juya halin Musulinci na kasar mai rasuwa.

Ministan Al’adu na Iran Abbas Salehi ya sanar da cewa kimanin ‘yan jarida 600 da wakilai daga kafafen yada labarai na kasashen waje za su halarci jana’izar marigayi Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, wadda aka shirya gudanarwa daga ranar 4 zuwa 9 ga watan Yuli.

Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, Salehi ya yi cikakken bayani game da shirye-shiryen da ma’aikatarsa ​​ta yi don jana’izar, ciki har da shirye-shiryen kafofin watsa labarai, fina-finai, da al’adu da suka shafi taron.

“A bangaren kafofin watsa labarai, kimanin ‘yan jarida 600 da wakilai daga kafofin watsa labarai na kasashen waje da na cikin gida za su halarci jana’izar domin a isar da wannan taron ga al’ummar duniya,” in ji shi.

Kafin hakan dama Hukumomi a Iran sun ce wakilai daga kasashe 90 ne ake sa ran zasu halarci tarurukan jana’izar Jagoran juyin juya halin Musulinci na kasar mai rasuwa Shahid Ayatollah Seyyed Ali Khamenei.

Baya ga hakan ana sa ran mutum miliyan 20 su halarci tarurukan.

An tsara gudanar da tarukan ban kwana da mirigayin daga ranar 4 zuwa 9 ga watan Yuli a biranen Tehran, Qom, da kuma Mashhad.

Za’a binne Ayatollah Ali Khamenei a birnin Mashhad ranar Alhamis 8 ga watan Yuli, wacce aka ayyana a matsayin ranar zaman makoki a fadin kasar.

Gwamnatin Iran ta sanar cewa za a rufe babban birnin kasar, Tehran, a ranar Talata 6 ga wata, domin saukaka gudanar da tarurukan jana’izar da kuma bai wa masu makoki damar fita daga birnin cikin sauki bayan halartar tarukan.

A Iraki makobciyar kasar ma an tsara tarukan tunawa da mirigayin a biranen Bagadaza, Kazmin, Karbala da Najaf.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted