Ma’aikatar Tsaron Kasar Iran ta jaddada cewa: Babu wani batun gudanar da shawarwari kan karfin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki na Iran
Mukaddashin Ministan Tsaro da Harkokin Jiragen Sama na Iran, Birgediya Janar Seyyed Majid Ibn Reza, ya jaddada cewa: Karfin tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran, makami mai linzami, da jiragen sama marasa matuki ciki sun zama ja layi ga tsaron kasa, yana mai jaddada cewa: Babu wani zaman shawarwari da za a yi kansu, kuma ba za a yi shawarwari kansu ba.
A cikin wani rubutu da ya yi a dandalin “X” bayan ganawarsa da mambobin Kwamitin Tattalin Arziki na Majalisar Shawarar Musulunci (wato Majalisar Dokokin Iran), Ibn Reza ya bayyana cewa ya yi bitar girma, nasarori, da halaye na “YaĆ™in Ramadan” a lokacin taron, yana mai jaddada cewa karfin tsaron Iran ya zama ginshiki na kare tsaron kasa.
Ya kara da cewa: Iran na ci gaba da karfafa karfin tsaronta, makami mai linzami, da jiragen sama marasa matuki ciki, yana mai lura da cewa ci gaban wadannan karfin zai ci gaba da dogaro da albarkatun kasa da karfinsu na cikin gida.
Ya sake nanata cewa karfin tsaron, makami mai linzami, da jiragen sama marasa matuka na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya zama ja layi ga tsaron kasa, yana mai jaddada cewa ba za a yi shawarwari kansu ba ko kuma neman jin matsayinsu daga kowane bangare ba.