Iran ta musanta cewa ta gudanar da tattaunawa da Amurka a birnin Doha na kasar Qatar
Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran kan Harkokin Shari’a da Ƙasashen Waje, Kazem Gharibabadi, ya musanta rahotannin da ke ikrarin cewa: An yi wani taro tsakanin wakilan Iran da Amurka a birnin Doha na Qatar.
Gharibabadi ya tabbatar da cewa: Ayyukan tawagar Iran sun takaita ne kawai ga halartar tarurrukan bangarori uku da masu shiga tsakani na Qatar da Pakistan don ci gaba da aiwatar da Yarjejeniyar Fahimtar juna da aka sanya wa hannu a Islamabad.
Mataimakin Ministan Harkokin Wajen ya ƙara da cewa: Tarurrukan tawagar Iran sun takaita ne kawai ga tarurrukan haɗin gwiwa na ɓangarori uku da wakilan Qatar da Pakistan don sa ido kan aiwatar da tanade-tanaden Yarjejeniyar Fahimtar juna ta birnin Islamabad, musamman waɗanda suka shafi Lebanon da kuma sakin kadarorin Iran da aka tsare.
Abin lura a nan shi ne cewa: Tawagar fasaha ta Iran, ƙarƙashin jagorancin Gharibabadi, ta gudanar da tarurrukan da bangarori uku a ranar Laraba a Doha tare da masu shiga tsakani na Qatar da Pakistan don ci gaba da aiwatar da Yarjejeniyar Fahimtar Juna ta Islamabad.