Ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta sanar cewa an kamala tattaunawa daban-daban tsakanin wakilan Iran da Amurka a birnin Doha, yayin da aka shirya ci gaba da wasu tattaunawar nan gaba bayan jana’izar jagoran Iran mai rasuwa.
Wannan ci gaba ne akan aiwatar da batutuwan da suka shafi yarjejeniyar fahimtar juna da Islamabad ta shiga tsakani wadda aka sanya wa hannu tsakanin Tehran da Washington a watan da ya gabata.
Kafin hakan Mataimakin Ministan Harkokin Waje da Shari’a da Harkokin Kasashen Waje na Iran, Kazem Gharibabadi ya ce tarurrukan Doha sun mayar da hankali kan aiwatar da yarjejeniyar.
Ya soki ci gaba da keta yarjejeniyar musamman a sashe na 1 game da dakatar da yaki a Lebanon, da rahotannin kokarin Amurka na ƙarfafa kayan aiki da sojoji a yankin, da kuma wasu kalamai na barazana da tsoma baki daga jami’an Amurka.
A ranar 18 ga Yuni ne shugaban Iran Masoud Pezeshkian da shugaban Amurka Donald Trump suka sanya hannun kan yarjejeniyar fahimtar juna daga nesa, a shiga tsakanin Pakistan da Qatar domin kawo karshen yakin da Amurka da Iran suka shelenta kan Iran a ranar 28 ga watan Fabarairu.