Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta ce kasar za ta dauki fansa akan kisan jagoran juyin juya na kasar Shahid Ayatollah Sayyed Ali Khamenei.
Za a hukunta wadanda suka aikata kisan Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, da kuma mutanen Iran a lokacin da ya dace.
“Wadannan su ne kalmomin da Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mohammad Bagher Zolghadr, ya wallafa a shafinsa na X, yayin da kasar ke shirin gudanar da jana’izar Jagoran da ya yi shahada.
Kyawayen halaye, darusa da tsayin daka da muka kowa daga mirigayin zasu ci gaba da wanzuwa har abada inji jam’in.
Wadanda suka ba da umarni, za su fuskanci hukunci,” in ji shi.
Da yake bayyana jana’izar Jagoran a matsayin “wani muhimmin lokaci na tarihi,” jinin Jagoran zai haskaka hanyar gaskiya zuwa ga nasara ta karshe da kuma yaki da girman kai.
Yana kira ga al’ummar Iran da su shiga cikin jerin gwanon jana’izar marigayi Jagoran, yana jaddada cewa wannan jana’izar ba wai kawai bikin makoki ba ne, za kuma su kasance bukukuwan mubayi’a da biyayya na jama’a” ga sabon Jagora, Ayatollah Seyyed Mojtaba Khamenei.