Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran ya bayyana cewa: Iƙirarin da ake yi game da masu sa ido na hukumar Makamashin nukiliya shiga wuraren da aka kai harin bam ƙarya ne
Kakakin Majalisar Shawarwarar Musulunci (wato Majalisar Dokokin Iran) ya musanta rahotannin da ke cewa: An bai wa masu binciken Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) damar shiga wuraren da aka kai hare-haren bama-bamai a cikin cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran.
Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Iran ta bi shawarar da Majalisar Tsaron Kolin Kasar ta yanke na hana gudanar da bincike a waɗannan wuraren.
A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin, Qalibaf ya bayyana cewa: Tattaunawar da aka yi a Zurich ta haifar da hanzarta sakin kadarorin da aka tsare na Iran da kuma dakatar da wasu takunkumai da aka kakaba mata. Ya kara da cewa, “Da ba a shiga wannan zagayen tattaunawa ba, da wasu sun yi tambaya game da makomar sharuddan da Iran ta gindaya.”
Ya kuma kara da cewa: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, a cikin sakonsa na baya-bayan nan, ya yi nuni cikin hikima cewa: Mutane da shugabanni suna jiran cikan sharuddan yarjejeniya. Sai Qalibaf ya yi tambaya cikin bacin rai cewa: “Ganin waɗannan yanayi, ta yaya ba zan bi waɗannan sharuɗɗan ba?” Akwai waɗanda ba sa ba wa ƙasar taimako, ko ta diflomasiyya a ƙasa, amma sai Iran ta kasance a shirye take ta bi dukkan hanyoyin amincewa da su.