Tsohon jami’in diflomasiyyar Pakistan ya bayyana cewa: Kokarin makircin Amurka da Isra’ila kan Iran ya gaza
Tsohon Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Pakistan, Aizaz Ahmad Chaudhry, ya yi ikirarin cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ce ke kan gaba wajen tunkarar hare-haren waje. Ya jaddada cewa kokarin Amurka da Yahudawan Sahayoniyya na kin jinin Iran ya gaza, kuma dole ne Amurka da Isra’ila su fahimci cewa hanya daya tilo da za su fita daga rikicin ita ce komawa ga Yarjejeniyar Fahimtar Juna don kawo karshen yakin.
Kamfanin dillancin labaran “IRNA” ya ruwaito a ranar Laraba cewa: Jami’in diflomasiyyar Pakistan ya bayyana a wata hira da wani tashar talabijin ta Pakistan cewa: Dole ne Amurkawa su fahimci cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kafu sosai kuma yunkurinsu na mamaye Iran ya gaza.
Chaudhry ya kara da cewa: Amurka, tare da Yahudawan Sahayoniyya, sun yi aiki don karfafa kungiyoyin ‘yan aware da kuma tayar da hankalin masu adawa da Iran a kasashen waje; duk da haka, duk wadannan kokarin ba su haifar da wani sakamako ba, kuma juriyar Iran ta ci gaba da kasancewa a tsaye. Saboda haka, dole ne su canza hanyarsu.