IRGC: Iran Zata Ci Gaba Da Shirinta Na Makamashin Nukliya

Iran zata ci gaba da gudanar da shirinta na makamashin nukliya ta zaman lafiya da gaske, duk tare da kokarin da makiya suka yi na

Iran zata ci gaba da gudanar da shirinta na makamashin nukliya ta zaman lafiya da gaske, duk tare da kokarin da makiya suka yi na lalata shirin.

Kamfanin dillancin labaran Tesnim na kasar Iran ya nakalto mataimakin babban kwamandan rundunar ta IRGC Manjo Janar Mostafa Izadi yana fadar a wani taro na tunawa da marigayi Imam Sayyid Aliyul Khaminaei(q) shahidi.

Iazadi ya ce makiya sun shigo kasar Iran tare manya manyan manufofi wadanda suka hada da kifar da gwamnatin kasar, yayyanka ta da kuma kawo karshen shirin makamashin Nukliya na kasar, a lokacin yakin sun yi kokarin shiga cibiyar makamashin nukliya ta kasar dake kasar Esfahan amma suka kasayin hakan.

Manjo janar Izadi ya ce , iran zata ci gaba da shirinta na makamashin nukliya, don neman ci gaban ilmi da kuma amfani mai yawa dake cikin shirin. Wannan kuma shi ne hanya zuwa daukaka da kuma karfi a duniya.

Yace bukatan Amurka a kadar Iran suna da yawa, amma sun kasa cimma ko da guda daga cikinsu, daga ciki har da kawo karshen kawayen Iran a yankin.

Daga karshe ya ce JMI ta tsallaka dukkan matsaloli tare da taimakon All..da kuma jagoranci mai kyau na Imam Shahidimmu. Yace ya zuwa yanzu mun fara ganin sauye sauye da dama a duniya, wadanda suke nuna rauni da kuma dushewar karfin Amurka a duniya.

Yace a halin yanzu sojojin Iran ne suke iko da mashigar ruwa ta Hurmuz kuma wacce ta kasance mashiga ga bukatun duniya na makamshi mai yawa. Hakama wasu kayaki masu muhimmanci a cikin kasashen yankin.

A fagen yankin kuma kawayen Iran ne suke iko da wasu waurare masu muhimmanci kamar babul mandab na kasar yemen da tekun red sea.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted