Qalibaf: Hormuz Zata Ci Gaba Rufewa

Har Zuwa Lokacinda Trump Ta Amince Da Sharuddan Iran Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibaf ya sake nanata cewa mashigar ruwa ta Hurmuz

Har Zuwa Lokacinda Trump Ta Amince Da Sharuddan Iran Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibaf ya sake nanata cewa mashigar ruwa ta Hurmuz zata ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa lokacinda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya amince da takardan fahintar juna da ya rattabawa hannu a Islamabad.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a jiya Talata ya kuma kara da cewa, Iran tana aiki ne bisa umurnin jagoran juyin juya halin musulunci Aya. Sayyid Mojtaba Khaminaei, na tabbatar da cewa Amurka ta mutunta hakki da bukatun mutanen kasar Iran.

Yace Iran zata kai ga wadan nan bukatu ne ta hanyar amfani da karfin soje da kuma hanyar diblomasiyya.

Ya ce, Iran zata takurawa Amurka sai ta koma kan takartan fahintar juna ko MOU ta Islamabad wacce ta tattara dukkan bukatun JMI a wannan yakin. Ya ce MOU ta Islamabad ta hada da sakin dukkan kudaden kasar Iran wadanda Amurka ta hana a tabasu a bakunan da dama a duniya, dauke mata dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar, tun fiye da shekaru 40 da suka gabata. Dukewa iran dukka takunkuman tattalin arziki kan man kasar, da kuma kawo karshen yaki ta yanda Amurka ba zata taba zama barazana ga tsaron kasar Iran ba.

Qalibaf ya bayyana cewa da farko Amurka ta amince da bukatun kasar Iran ne ba bisa sonta ba sai dai don tana son a kawo karshen budewa juna wuta, amma a lokacinda ta sami hakan sai ta fara saba masu daya bayan daya don rage kunyar rashin nasara da tayi a yakin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted