Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyaa cewa: Iran ta yi watsi da zarge-zargen da Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi kanta
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da ikirarin Hadaddiyar Daular Larabawa game da harba makamai masu linzami guda biyu daga Iran zuwa kan kasarta.
Baqa’i ya nuna takaici kan zargin da Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi wa Iran, yana mai cewa irin wannan dabi’a ta saba wa ka’idar kyakkyawar maĈwabtaka kuma tana kawo cikas ga kokarin da ake yi na karfafa aminci tsakanin kasashen yankin da kuma hana karuwar tashe-tashen hankula.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje ya yi kira ga dukkan bangarorin yankin da su guji yin zarge-zarge marasa tushe ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, tare da la’akari da yanayin da ake ciki a yanzu sakamakon munanan ayyukan Amurka da Yahudawan Sahayoniyya kan zaman lafiya da tsaron yankin, musamman ganin tarihin ayyukansu da dama na karya kimiyya.