Araqchi: Kallon Iran A Matsayin Kasa Mai Rauni Ya Kawo Karshe

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa tunanin Iran kasa ce mai rauni bayan yakin da Amurka ta dorawa kasar ya kuma

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa tunanin Iran kasa ce mai rauni bayan yakin da Amurka ta dorawa kasar ya kuma bace daga tunanin mutane,

saboda a aikata ce Iran ta nuna cewa it aba mai rauni bace, kuma duk duniya ta amince da haka.

Don haka wannan tunanin ya fice daga kwakwalen mutane.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Araqchi yana fadar haka a nan Tehran ya kumakara da cewa Iran kafin yaki ba daya bane da Iran bayan yaki,

Iran kafin yaki ana daukarta kasa mai rauni, amma Iran a bayan yaki daya daga cikin kasashe masu karfi a duniya ce.

Don haka hatta tsarin tafiyar da ayyukanta na diblomasiyya a duniya zai sauya.

Aragchi ya fadawa Tasnim kan cewa, yakin Amurka da HKI kan kasar Iran a farkon wannan shekarar ya sauya tunanin kasashen duniya dangane da kasar.

Ya ce a lokacinda Trump ya fara kaiwa kasar Iran hare hare yana bukatar mika wuya ne kawai, yana bukatar kwace kasar rarrabata, sauyin shugabanci da wasu al-amura da dama , yake yaken cikin gida amma ya kasa samun ko guda daga cikinsu.

Banda haka ma sun rasa mashigar ruwa ta Hurmuz wacce ta kasance a bude kafin yakin. Banda haka sun yi kokarin kawo karshen yakin ma suka kasa.

Banda haka Iran ta shaida musu tun kafin a fara wannan yakin kan cewa zasu kai hare hare kan sansanonin Amurka a kasashen yankin daga inda suke kawo mana hare hare. 

Amma suka yi kunnen uwan shegu da gargadin.

Ministan ya kammala da cewa, mai yuwa sake tattaunawa da shugaban Trump nan gaba shi ne zai kawo karshen yakin bayan ya amince da dukkan sharuddan da Iran ta shimfida.

Sannan yace shugaban Kasa Masuod Pezeshkiyan ne ya bukaci Muhammad Bakir Qalibof ya jagoranci tawagar tattaunawa da makiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted