Farashin Kayan Abinci Ya Sake Hauhawa A Sassan Najeriya

duk da mataken da gwamnatin naijeriya take dauka amma ana samun hauhawan farashin kayan abinci

Rahotanni sun bayyanan  cewa duk da sabbin matakan da gwamnatin Najeriya take ikirarin dauka a kokarin sassauta tsadar rayuwa ga ƴan kasar wajen bunkasa samar da abinci a cikin gida allaluma na nuni da cewa farashin kayan abinci ya sake hauhawa a watan jiya na Yuli idan an kwatanta da yadda farashin ya ke a watan Yuni, lamarin da ke sake jefa jama’ar kasar mafi karfin tattalin arziki a Afrika.

Alkaluman da hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta fitar game da hada-hadar watan Yulin da ya gabata ya nuna cewa hauhawar farashin kayakin abinci ya tsaya a maki 20.31 wanda ke nuna sassauci idan an kwatanta da yadda farashin ya ke a irin wannan lokaci a bara wato watan Yulin 2025.

Alkaluman na NBS ya nuna cewa hauhawar farashin ya karu da kashi 5.56 a watan Yuli fiye da hauhawar da aka gani a watan Yuni na kashi 3.75, banbancin da ke nuna karuwar kashi 1.82.

Rahoto na daban ya yi nuni da cewa dimbin ƴan Najeriya basu ga  tasirin shirye-shiryen da gwamnatin ke yi na sauƙaƙa rayuwa ba. Sai dai rahoton ya ce matsi da tsadar rayuwa ta saukaka a watan Yuli zuwa kashi 15.43 sabanin kashi 15.91 da aka gani a watan Yuni, wanda ke wakiltar raguwar kashi 0.48.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted