Iran: Jami’an Diblomasiyyar Faransa Biyu ‘Ba’a bukatarsu ‘

Gwamnatin JMI ta bada sanarwa a jiya Talata kan cewa bata bukatar samuwar jami’an diblomasiyyar kasar Faransa guda biyu a cikin kasar. Kamfanin dillancin labaran

Gwamnatin JMI ta bada sanarwa a jiya Talata kan cewa bata bukatar samuwar jami’an diblomasiyyar kasar Faransa guda biyu a cikin kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar na bada wannan sanarwan, ta kuma kara da cewa wadannan jami’an diblomasiyyar kasar faransa guda biyu, sun halarci wani taro a cikin watan Yulin da ya gabata tare da wadanda ake tuhuima da hannun a shigo da yan ta’adda daga kasashen waje don kifar da gwamnatin kasar a farkon wannan shekarar.

Taron wanda suka yi shi a asirce a cikin kasar, basu san cewa ma’aikatan leken asiri na kasar na binsu ba. Ma’aikatar ta bayyana cewa laifin da wadannan jami’an diblomasiyyan kasar faransa suka yi ya sabawa dokokin kasa da kasa, da kuma taron Vienna na al-amuran diblomasiyya na shekara ta 1961.

Daga karshe bayanin ya kammala da cewa Iran ta dauki wannan matakin ne bayan da gwamnatin kasar Faransa ta kasa daukar matakai don gyara al-amura, bayan an fallasa masu laifin wadannan jami’an diblomasiyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted