Kungiyar malaman jami’o’ii a tarayyar Najeriya ASUU ta bayyana damuwarta da yanda wasu jami’o’ii masu zaman kansu a kasar suka maida ma’aikatan Jami’o’ii malamai ba tare da bin hanyoyin da suka dace na yin haka ba.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto shugaban kungiyar Prof. Christopher Piwuna yana fadar haka a ranar Jumma’a ya kuma kara da cewa, kungiyarsa bata adawa da yin hakan, amma jami’o’iin basu yishi kamar yanda ya dace ba.
Shugaban na ASUU ya bukaci hukuma mai kula da Jami’o’ii a kasar wato ‘ the National Universities Commission (NUC)’ yakamata ta yi aikinta don ganin ta dawo da doka da oda a cikin tsarin tafiyar da jami’o’I a kasar.
Kungiyar har’ila yau tayi kira da shuwagabannin Jami’o’I su kula da wadan nan matsaloli su kuma gyara su don kyautata ilmin jami’o’ii a kasar.