Qalibaf: Iran Ba Zata Yi Wata Tattaunawa Kafin Amsa Sharuddanta

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Ba za a yi wata tattaunawa ba kafin a cika sharuɗɗa bakwai na Iran Shugaban Majalisar

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Ba za a yi wata tattaunawa ba kafin a cika sharuɗɗa bakwai na Iran

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran wato Majalisar Dokokin kasar Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Ba za a ɗauki wani mataki ko tattaunawa ba kafin a cika sharuɗɗa bakwai na Iran, kuma Iran a shirye take ta mayar da martani mai ƙarfi da kuma sauya fagen daga idan maƙiya suka yi kuskure.

A cewar kamfanin dillancin labaran Iran Mehr, Kakakin Majalisar Dokokin Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada a ranar Talata, 24 ga watan Nuwamban wannan shekara ta 2026, a lokacin jawabinsa kafin fara zaman Majalisar, cewa: Matsayin Iran kan tattaunawa da Amurka a bayyane yake kuma ba ya canzawa, yana mai jaddada cewa: Babu wani mataki ko tattaunawa da za a yi kafin a cika sharuɗɗa bakwai na Iran.

Qalibaf, wanda ke magana a lokacin Makon Dakarun Sa-Kai na Basij, ya lura cewa: Wannan cibiya ta gado ce ta marigayi Imam Khomeini da mabiyansa masu himma, yana mai bayyana cewa ta wuce ra’ayin ƙungiya ta zama babbar hanyar sadarwa ta imani, kwarin gwiwa, da gogewa da ke fitowa daga zuciyar al’umma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted