Tawagar Burkina Faso ta halarci taron Jana’izar Ayatollah Seyyed Ali Khamenei

Burkina Faso ta halarci tarurukan jana’izar Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei. Ministan Harkokin Wajen kasar ne ya jagoranci tawagar

Burkina Faso ta halarci tarurukan jana’izar Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei.

Ministan Harkokin Wajen kasar ne ya jagoranci tawagar Burkinabe, wanda ya wakilci shugaban kasar, Kyaftin Ibrahim Traoré.

Ministan Harkokin Wajen kasar Karamoko Jean Marie Traoré ya yi wa jama’a da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta’aziyyar Burkina Faso.

Sannan ya sanya hannu kan littafin ta’aziyyar, yana mai girmama “Jagoran wanda tasirinsa na siyasa da ruhaniya ya wanzu a duniya”

A gefen halartarsa ​​a tarururukan jana’izar ministan harkokin wajen na Burkina Faso ya gana da takwaransa na Iran, Abbas Araghchi.

Ganawar manyan Jami’an biyu wani bangare ne na ci gaba da kokarin karfafa dangantakar kasashen biyu tsakanin Burkina Faso da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Bangarorin sun tabo batutuwa da dama na ƙarfafa haɗin gwiwa, musamman a fannonin tsaro, diflomasiyya, da kuma a fannin tattalin arziki da kasuwanci.

Mista Karamoko Jean Marie Traoré ya yi amfani da zuwansa a Tehran don yin tattaunawa da wasu takwarorinsa na Afirka, musamman daga Congo, Namibia da Masar.

Jana’izar Shahid Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ta tattaro wakilai kusan 100 na kasashen waje, ciki har da wasu daga Afirka, Asiya, da Gabas ta Tsakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted