Miliyoyin jama’a sun fita a titunan Tehran domin ban kwana da Ayatollah Seyyed Ali Khamenei

A Tehran Miliyoyin jama’a ne suka fito akan titunan Tehran a safiyar yau domin ban kwana da Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar, Ayatollah

A Tehran Miliyoyin jama’a ne suka fito akan titunan Tehran a safiyar yau domin ban kwana da Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, a ci gaba da tarurukan jana’iza da ake wa mirigayin.

Titunan babban birnin Tehran, sun kasance cike makil da jama’a sanye da bakaken kaya dauke da jajayen tutoci da hotunan miriyin a yayin da ake zazagayawa da gawarsa da ta ‘yan uwansa hudu da sukayi shahada tare a a harin Amurka da Isra’ila.

Masu shirya taurukan sun ce an kwashe awa 10 zuwa 12 ana zagayawa da akwatinan mirigayen a kusan kilomita goma da ya hada manyan tutuna da wuraren taron jama’a a birnin.

Jama’a da suka taru suna bugun kirjinsu cikin jimami, na kiran a dau fansa akan kisan da akayi wa jagoran.

Bayan zagayen da akayi a Tehran a gobe Talata za’a kai gawawakin a binrin Qom inda cen jama’a zasuyi ban kwana da shi.

Sai kuma ranar Laraba inda za’a gudanar da irin wadanan tarurukan a biranen Najaf da Karbana, kafin daga bisani a sake dawowa Iran a Birnin Mashad inda za’a binne shi a ranar Alhamis.

Kafin hakan dama a ranar Lahadi, Babban Ayatollah Jaafar Sobhani ya jagoranci sallar jana’izar tsahon Jagoran , tare da surukinsa, Dr. Mesbah-ol-Hoda Bagheri-Kani, da surukarsa, Zahra Haddad-Adel, da jikarsa, Zahra Mohammadi Golpayegani (mai watanni 14), da ‘yarsa, Seyyedeh Boshra Hosseini Khamenei.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted