Shugabannin kasashen Larabawa sun bukaci da a gaggauta tsagaita bude wuta a zirin Gaza.
Bayan wani taronsu a Bahrain, jiya Alhamis, Shugabannin kasashen Larabawa sun ce suna son a girke dakarun wanzar da zaman lafiya a yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta mamaye har sai an fara aiwatar da yarjejeniyar kafa kasashe biyu, wato Isra’ila da Falasdinu, domin warware rikicin da aka shafe shekaru da dama ana yi.
A cikin sanarwar karshen taron nasu na Manama, shugabannin kasashen Larabawa sun kuma amince da kiran da aka yi na “taron kasa da kasa karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya” don warware rikicin “bisa hanyar samar da kasashe biyu”.
Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu na adawa da kafa kasar Falasdinu, wanda gwamnatin Amurka da kasashen kungiyar Tarayyar Turai ke kallon shi a matsayin mafita daya tilo da za a iya magance rikicin.
Shugabannin Larabawan sun ce “Muna bukatar tsagaita bude wuta na dindindin a Gaza, da kawo karshen duk wani yunkuri na tilastawa falasdinawa yin hijira, da kawo karshen duk wani nau’i na kawanya “don samun isar da kayan agaji,”
Taron na kasashen Larabawa ya zo a daidai lokacin da Isra’ila ke “kara tsananta” ayyukanta na kasa a Rafah da ke kudancin zirin Gaza, duk da gargadin da kasashen duniya suka yi kan hakan abinin mai cike da falasdinawa dake zaman mafaka.