Sojojin Yemen sun kai hari kan tashar wutar lantarki ta Shuqaiq da tashar jiragen ruwa ta Jizan a Saudiyya
Kakakin Rundunar Sojojin Yemen ya sanar da kai hare-hare kan tashar wutar lantarki ta Shuqaiq da tashar jiragen ruwa ta Jizan a kasar Saudiyya.
Kamfanin Dillancin Labaran Mehr ya ruwaito cewa: Janar Yahya Sari’e, kakakin Rundunar Sojojin Yemen, ya sanar da cewa: “Da taimakon Allah, rundunar sojin Yemen ta kai wani hari na musamman kan tashar wutar lantarki ta Shuqaiq da tashar jiragen ruwa ta Jizan. Waɗannan hare-haren an kai sune kai tsaye kan wuraren, inda suka yi barna mai yawa.”
Ya ƙara da cewa: “Wannan harin ya zo ne a matsayin martani ga harin da makiya Saudiyya suka kai wa tashoshin wutar lantarki na Sa’ada da Mocha da kuma harin da aka kai a safiyar yau a tashar jiragen ruwa ta Hodeidah.”
Yahya Sari’e ya kuma bayyana cewa: “Suna tabbatar wa makiya Saudiyya cewa: Duk wani hari da aka kai wa tashar jiragen ruwa ta Hodeidah ko tashoshin wutar lantarki za a mayar da martani kai tsaye kan tashoshin jiragen ruwa da tashoshin wutar lantarki ta Saudiyya.”